Wasu ma’aikata a jihar Borno sun koka kan yadda suke karɓar ƙasa da 10,000 a matsayin albashi, inda kwamishinan ilimi na jihar, Injiniya Lawan Abba Wakilbe ya shaida wa BBC dalilan da suka sa ake biyan wasu ma'aikatan albashin da 'bai taka kara ya karya ba'.